Gujba: 'JTF ta kama 'yan Boko Haram 15'

Image caption Sojan Najeriya suna sintiri

Rundunar hadin gwiwa ta samar da tsaro a jihar Yobe, wato JTF ta ce, ta kama 'yan kungiyar Boko Haram goma sha biyar yayin samamen da suka kai wani sansani a ƙoƙarin bankaɗo wadanda suka kashe ɗalibai kusan hamsin a ƙarshen makon da ya gabata.

JTF ta ce, ta yi kamen ne a wani sansani da ta gano na 'yan ƙungiyar ta Boko Haram.

Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne dai suka hallaka dalibai kusan hamsin a kwalejin koyon aikin gona ta jihar Yobe a Gujba.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake kai hare-hare a makarantu a jihohin Yobe da ma Borno.