An yi jana'izar marubuci Awoonor a Ghana

Marubucin wakoki na Ghana, Kofi Awoonor
Image caption Marubucin wakoki na Ghana, Kofi Awoonor

A Ghana an yi addu'o'in jana'izar shahararren marubucin wakokin adabin nan, Kofi Awoonor wanda aka kashe a harin rukunin shaguna na Nairobin a Kenya.

Mutane da yawa cikin har da manyan jami'an gwamnati ne suka halarci jana'izar a wani kauye dake wajen birnin Accra, babban birnin kasar ta Ghana.

An yi addu'oin cikin tsauraran matakan tsaro, kuma za a kona gawar ta Mr. Awoonor ne, kafin a kai tokar kauyensu.

Marubucin na Ghana ya yi zamani da fitaccen marubucin Najeriyan nan Chinua Achebe.