Mutane 82 sun mutu a gabar tekun Italiya

Image caption Masu aikin ceto ne kokarin gano gawarwakin mutane 200

Jami'an tsaro dake kula da teku sun ce an samu gawarwaki sama da 82 bayan wani jirgin ruwa dauke da 'yan ci rani daga Afirka ya kama da wuta ya kuma nutse a tsibirin Lampadusa.

Har yanzu ba'a gano kimanin mutane 200 ba.

Praministan kasar Italiya, ya kira lamarin a matsayi wani babban abun bakin ciki.

Daga cikin mutanen da suka mutun har da mata masu juna biyu da kuma kananan yara.

Jami'ai a Italiya sun sun an samu ceto sama da mutane 150 daga cikin ruwa kuma ana ci gaba da laluban wasu.

Mai rike da mukamin magajin garin ta zubda hawaye lokacin da wadanda suka tsira da ransu suka bada labarin yadda aka kunna wata 'yar karamar wuta dan neman taimako saboda jirgin ya samu matsala.

Karin bayani