Mutane 16 sun rasu a hadarin jirgin sama a Lagos

Image caption Hadarin jirgin sama a Lagos ya zama ruwan dare

Mutane akalla 16 sun mutu a hadarin karamin jirgin sama da ya auku a birnin Lagos dage kudancin Najeriya.

Jirgin na kamfanin sufurin jiragen sama na Associated Airlines, wanda ke dauke da mutane 27 , ya fadi ne jim kadan bayan tashinsa sannan kuma ya kama da wuta.

Jirgin yana kan hanyarsa ce ta zuwa Akure babban birnin jihar Ondo, kuma yana dauke da gawar tsohon gwamnan jihar ta Ondo, Olusegun Agagu, wanda ya mutu a kwanan baya.

Wani kakakin ma'aikatar sufurin jiragen saman Najeriya, ya ce akwai mutanan da suka tsira da ransu kuma ana cigaba da aikin ceto.

Najeriya dai ta yi kaurin suna dangane da hadarin jiragen sama, kuma rahotanni sun nuna cewa akalla mutane dubu daya suka rasu a hadarin jirgin sama a Najeriyar a shekaru 30 din da suka wuce.

Karin bayani