An kashe akalla mutane hudu a Masar

zanga zangar kasar Masar
Image caption Ban Ki-Moon ya ce ya damu da zanga zangar Masar kuma ya nemi a kwantar da hankali

Akalla mutane hudu ne suka mutu sakamakon harbin bindiga a babban birnin Masar, Alkahira.

Inda jami'an tsaro suke dauki-ba-dadi da daruruwan magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi.

Masu zanga zangar dai na kokarin isa tsakiyar dandalin Tahrir ne cibiyar zanga zangar Masar.

Su kuma jami'an tsaron ke kokarin hana su kai wa wurin ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye tare da harbi.

A fadin kasar ta Masar an jikkata akalla mutane 40 kuma.