Nukiliya: 'Iran za ta zama karfen kafa'

Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Image caption Iran ta sha jaddada cewa shirin nukiliyarta ta zaman lafiya ce

Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi gargadin cewa, idan Iran ta mallaki makaman nukiliya, to za ta zama karfen kafa kamar Koriya ta Arewa.

Mr. Netanyahu ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, inda ya ce sabon shugaban Iran, Hassan Rouhani ba zai iya sauya shawarar da jagoran addini na kasar Ayatollah Ali Khamenei ya dauka ba.

Mr. Netanyahu ya ce yana fatan za a cimma kawo karshen batun kera makaman nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya, amma a cewarsa maslaha ta gaskiya, ba wai ta karya ba.

Firai ministan ya kuma bayyana cewa mutanen Iran sun cancanci gwamnatin da ta fi wacce suke da ita a yanzu.