Kisan Malami ya janyo tarzoma a Mombasa

Mutane a kusa da motar da aka kashe Malam Ibrahim Rogo
Image caption Kisan na zuwa ne makonni kadan bayan harin rukunin shaguna na Westgate a Nairobi

Tarzoma ta barke a garin Mombasa na Kenya, bayan kammala sallar Juma'a, inda musulmai ke nuna rashin amincewa da kisan wani malamin addinin Musulunci, Ibrahim Rogo Omar.

Tarzomar ta kai ga kona mujami'ar salvation army, kamar yadda wani babban jami'in dan sandan ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP.

An harbe malamin da wasu mutane uku har lahira, a lokacin da suke tafiya a mota a ranar Alhamis da daddare a Mombasa.

Kisan Malam Ibrahim ya yi kama da ta malam Aboud Rogo Mohammed da aka yi a bara, wanda shi ma ya janyo tarzoma a garin dake da tashar jiragen ruwa.

Wasu Musulmai na zargin jami'an tsaro da aikata kisan malamin da ake zargi da alaka da kungiyar alshabab, zargin da suka musanta.