Majalisar Nijar za ta yi zama kan kasafin kudi

Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadu Issoufou
Image caption Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadu Issoufou

Majalisar dokokin Nijar za ta soma wani zama na watanni biyu, domin tattaunawa a kan sabon kasafin kudi na shekara ta 2014.

Sabon kasafin kudin da ya kai sefa biliyan 1800 ya dara na bara da kimanin biliyan 500 na sefa.

A taron ta na ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin ta yi na'am da shi, ta kuma ce da wannan kudin ne take son ci gaba da zartar da ayyukan da ta riga ta soma na shirin farfado da arziki da kyautata rayuwar jama'a.

'Yan majalisar dokokin za su mayar da hankali wajen bin kasafin kudin daki-daki su dubi kudaden da gwamnatin ta ware wa ko wane fanni domin bayar da shawarwarinsu a kai.