Ana bincike kan harbe wata mata a Amurka

Fadar Whitehouse ta Amurka
Image caption Fadar Whitehouse ta Amurka

Ana gudanar da bincike a Washington, bayan da 'yan sanda suka harbe wata mata da ta tsallake shingen binciken kofar shiga fadar White House da motarta.

'Yan sandan sun budewa motar matar wuta ne yayinda ta tunkari zauren majalisar dokoki a guje.

Wata yarinya 'yar shekara daya kuma da aka ceto daga cikin motar na samun kulawa a asibiti.

An yi harbin ne yayin da ake ci gaba da takaddama tsakanin 'yan jam'iyar Democrats da ta Republican a Washington game da kasafin kudi.