An kama wani jagoran al-Qaeda a Libya

Sojojin Amurka
Image caption Dan uwan shugaban na al-Qaeda ya ce matar jagoran ta ga lokacin da aka kama shi

Hukumomin Amurka sun ce sun kama wani jagoran kungiyar al-Qaeda na Libya.

An kama shugaban ne mai suna Anas al-Libi a Tripoli.

Ana neman mutumin mai shekara 49 bisa zargin hannu a harin da aka kai kan ofisoshin jakadancin Amurka a gabashin Afrika a 1998.

Daman an sanya ladan dala miliyan biyar ga duk wanda ya bayar da bayanan da zasu taimaka a kama shi.

Karin bayani