Torokon teku na shafar ceto a Lampedusa

Jirgin ruwan da ya nutse a tekun kusa da Lampedusa
Image caption Jirgin ruwan da ya nutse a tekun kusa da Lampedusa

Rashin kyaun yanayi a tsibirin Lampedusa ya sa ma'aikatan ceto sun kasa komawa ayyukan da suka fara na tsamo gawarwakin bakin hauren nan da suka nutse a teku a farkon makon nan.

Tun a jiya, Juma'a da yamma ne aka fara fuskantar wannan matsala, wadda ta kawo cikas ga aikin.

Ana fargabar cewa har yanzu akwai gawarwakin mutane dari biyu a cikin tekun.

Karin bayani