Maniyyata Hajji sun tsallake rijiya da baya

Filin jirgin sama
Image caption Jirgin mahajjata ya yi saukar gaggawa a Sakkwato

Wani jirgin sama dauke da maniyyata aikin hajji 'yan jirgin yawo, su kimanin dari hudu, ya yi saukar gaggawa a Sakkwato bayan tayoyinsa sun fashe.

Rahotanin da muka samu sun ce Jirgin na kamfanin Kabo ya tashi ne daga Kano.

Kuma an sauki maniyyatan a wani babban Otal da ke birnin Sakkwato.

Karin bayani