Mazauna garin Gwoza na zaman dar-dar

Harin Gwoza
Image caption Harin Gwoza

A Najeriya, al'ummar karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar sun koka game da zaman dar-dar da suke ciki sakamakon yawan hari da suka ce 'yan kungiyar jama'atu ahli sunna lidda'awati waljihad na kai musu.

Mazauna garin sun shaidawa BBC cewa 'yan kungiyar ta Boko haram sun kona makarantu, baya ga tare mutane da suke yi kuma akan hanya.

Wani mazaunin garin da ya gudu ya kuma nemi a sakaya sunan sa, ya shaidawa BBC cewa, ko a ranar asabar din da ta gabata wasu 'yan bindiga sun tare hanya inda suka tsaya adai-dai wani kauye mai suna Kirawa suka tare mutane idan sun ji kai dan Gwoza ne ko Bama sai su yanka ka.

Mutumin ya bayyana cewa, yanzu haka mutanen garin musamman matasa duk sun gudu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka taba kai hari garin na Gwoza ba, ko a watannin baya ma wasu 'yan bindiga sun kai hari kan gidan yarin garin inda suka kubutar da mutane da dama wadanda ke zaman gidan kaso.

Kazalika a kwanan baya ma an kai hari a Gujba da ke jihar Yobe a kan makaranta inda aka kashe dalibai kusan hamsin aka kuma kona azuzuwa.

Karin bayani