'Yan Nijeriya na cece-kuce kan taron kasa

Shugaba Jonathan na Nijeriya
Image caption Shugaba Jonathan zai shirya taron neman makomar kasar

Yayin da ake sa ran gobe Ltinin shugaban Nijeriya, Dr Goodluck Jonathan, zai kaddamar da kwamitin da ya kafa don shirya wani babban taro na kasa domin duba makomar kasar, jam'iyyar adawa ta People's Democratic Movement, PDM, ta soki matakin shirya taron da cewa wata dabara ce kawai da gwamnatin PDP ta bullo da ita domin lullube gazawarta.

To sai dai jam'iyyar PDPn ta musanta zargin da cewa kishin kasa ne ya sa ake kokarin kiran taron domin ciyar da kasa gaba, don haka kamata ya yi yan adawa su rika suka mai ma'ana.

A gefe daya kuma sauran 'yan nijeriya na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu, yayinda wasu ke goyon baya, wasu kuma gwasale shirin suke yi.

Karin bayani