An yi rikici tsakanin shi'a da sunni a Sokoto

Jami'an tsaron Nijeriya
Image caption Jami'an tsaron Nijeriya

Rahotanni daga garin Sokoto a jihar Sokoto na cewa an samu barkewar rikici tsakanin 'yan shi'a da wasu mabiya Sunni a cikin garin.

Duk da cewa ya zuwa yanzu babu rahotannin samun asarar rayuka, wasu da suka shaida lamarin sun ce an samu jikkata a sakamakon sare-sare.

Wasu da suka shaida lamarin sun ce rikicin ya barke ne lokacin da wasu matasa 'Yan sunni suka far ma 'yan Shi'a dake cikin jerin gwanon motoci, suna rakiya ga wasu 'yan uwansu da aka sako daga gidan kaso.

Hukumomin 'Yan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin, amma sun ce rikicin ya lafa.

Karin bayani