Fraiministan Canada zai kauracewa Kwamanwelz

Fraiministan Canada Stephen Harper
Image caption Mr Harper na nuna damuwa ne kan zargin cin zarafin dan'adam da ake yi wa Sri Lanka

Fraiministan Canada Stephen Harper ya ce yana sake duba tsarin tallafin kudin da kasarsa ke bai wa kungiyar kwamanwelz saboda cin zarafin dan'adam a Sri Lanka.

Canada ita ce kasa ta biyu da ta fi bai wa kungiyar kudade.

Mr Harper ya ce ba zai halarci taron kungiyar wadda galibi tsoffin kasashe renon Ingila ne a cikinta ba na gaba ba.

Taron da za a yi a Sri Lamka a watan Nuwamba..

Fraiminstan ya ce gwamnatin Sri Lanka har yanzu ba ta gudanar da bincike kan zargin azabtarwa da aka yi ba, a lokacin yakinta da 'yan tawayen Tamil Tiger.

Da kuma batun batarwa da cin mutuncin yan jarida na 'yan siyasa ba.

Sri Lanka ta yi watsi da batutuwan na Fraiministan tana mai cewa idan da akwai wasu batutuwa na cin zarafin jama'a to tana gudanar da bincike a kai.