Malala Yousufzai za ta shiga siyasa

Malala Yousufzai
Image caption Malala ta ce lokacin da aka harbe ta tana jiran motar makarantai taga titi ba mutane sosai

Yarinyar nan da 'yan Taliban suka harba a ka a Pakistan shekara daya da ta wuce ta ce tattaunawa da 'yan gwagwarmaya ce hanya daya ta cimma zaman lafiya.

A wata hira da ta yi da BBC Malala Yousufzai ta ce ta hanyar ilimantar da manyan gobe ne a Pakistan da Afghanistan za a iya magance matsalar bin tsattsauran ra'ayi.

Malala mai shekara 16 ta kuma bayyana sha'awarta ta komawa Pakistan ta shiga siyasa.

Ta ce za ta ci gaba da gwagwarmayar bayar da ilimi kyauta kuma dole.

A kasar da sama da yara miliyan 25 ba sa zuwa makaranta.

Karin bayani