Kotu ta soke zaben Maldives

lokacin zaben maldives
Image caption Magoya bayan Mohammed Nasheed ba su ji dadin hukuncin kotun ba.

Kotun kolin Maldives ta soke zaben shugaban kasar da aka yi a watan da ya wuce ta kuma ba da umarnin gudanar da sabo.

Kotun ta yi wannan hukunci ne bayan da dantakarar da ya zo na uku a zaben Qassim Ibrahim ya shigar da kara yana zargin magudi.

Kotun ta ce sama da kuri'u dubu biyar ne aka yi magudinsu ta kuma bayar da umarnin gudanar da sabon zagayen farko na zaben ranar 20 ga watan nan na Oktoba.

Masu sanya idanu a zaben na duniya da suka hada da na India da kungiyar kasashen Turai da kuma Amurka sun yaba da zaben.

Zababben shugaban kasar na farko Mohammed Nasheed, wanda aka hambarar daga mulki.

A wani lamari da aka yi zargin juyin mulki ne ya samu nasarar kashi 45 cikin dari na kuri'un.