Taron yaki da rashawa na duniya a Najeriya

Shugaba Jonathan da takwarorinsa na Afrika
Image caption Yau za a fara wani taro na hukumomin Afrika masu yaki da cin hanci da rashawa a Abuja

A Najeriya, a yau (Litinin) ne ake sa ran hukumomin dake yaki da cin hanci da rashawa daga kasashe dabam-dabam na nahiyar Afirka za su fara wani taron mako guda a Abuja da nufin inganta ayyukansu, musamman ta fuskar hadin-gwiwa.

Jami'ai daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyi masu zaman kansu na daga cikin masu gabatar da kasidu a wajen taron.

Malam Nuhu Ribadu tsohon shugaban hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya, ya bayyana cewa taron yana da muhimmanci, domin idan aka samu hadin-kai na yaki da cin hanci da rashawa tsakanin kasashe, ba za a iya satar kudin wata kasa a kai wata kasar ba.

Malam Nuhu Ribadun yace cin hanci da handamar kudin kasa sune babbar matsalar Nijeriya, yana sukar lamirin Shugaba Jonathan wanda a kwanan baya yace, wadannan ba su ne matsalolin nijeriya ba.

Karin bayani