An kamalla jigilar maniyyata daga Najeriya

Image caption Masallacin Ka'aba a Makkah

A karon farko cikin shekaru masu yawa, an kamalla jigilar maniyyata daga Najeriya zuwa kasar Saudi Arabiya don gunarda aikin hajjin bana a kan lokacin da aka tsara.

Jirgin karshen wanda ya tashi daga Kano na dauke ne da jami'an hukumar kula da aikin hajjin Najeriya.

A shekarun baya, ana fuskantar matsaloli wajen jigilar alhazan abinda ke janyo hukumomin Najeriya su bukaci karin lokaci daga hukumomin Saudiyya don kammala diban maniyattan.

Kawo yanzu ba a samu wata matsala muhimmiya a lokacin tashin ba, kamar yadda ake samu a baya, musamman ma bara da aka samu matsalar batun dan uwa na kusa ga mata mahajjata.

Hukumomin hajjin na Najeriya dai na cewa a bana an samu nasarori sama da shekarun baya, abinda har ofishin jakadancin Saudiyya a Najeriya ya jinjinawa hukumomin hajjin bisa matakan da suka dauka.

Maniyatta daga Najeriya don hajjin bana sun kai mutane 76,000.

Karin bayani