'Yadda za a farfado da wasanni a Najeriya'

Image caption Malam Faruk Yarma

Shugaban hukumar wasanni a jihar Gombe dake arewacin Najeriya, Malam Faruk Yarma , ya bayyana cewar dole ne sai gwamnatoci sun baiwa wasanni mahimmanci don rage matsalar zaman banza a kasar.

A ziyarar da ya kawo ofishin BBC a London, Malam Yarma ya bayyana cewar akwai bukatar a kara yawan kudaden da gwamnati ke warewa wasanni a Najeriya don ci gaban matasa.

A cewarsa, kamata yayi a dakko batun daga tushe, wato kenan a soma horon matasa tun daga makarantun Firamare don zakulo hazikai a tsakaninsu.

Malam Faruk Yarma ya ce idan aka yi haka, kasar za ta dunkule waje guda ba tare da rarrabuwa ba.