An ga alamun nasara a yaki da Malaria

Image caption Sauro ke yada cutar Malaria

Kamfanin hada magunguna na Birtaniya, GlaxoSmithKline na bukatar amincewar hukumomi don samar da allurar riga kafin cutar Malaria a karon farko a duniya.

Gwajin da kamfanin ya gudanar ya nuna cewar an samu raguwar cutar daga yara a Afrika wadanda aka yi musu riga kafin.

Kwararru sun ce akwai alamun samar da riga kafin na farko a duniya saboda nasarorin da aka samu wajen gwajin.

Cutar zazzabin cizon sauro wato Malaria na hallaka dubun dubatar mutane a duniya baki daya.

Masana kimiya sun ce allurar riga kafin za ta iya kawar da cutar.

Allurar riga kafin mai suna RTS,S ta rage yawan yaran dake dauke da cutar da kusan rabi a cikin wadanda aka yi wa gwaji.

'Illar cutar'

Zazzabin Malaria na daga cikin cututtukan dake hallaka jama'a a duniya, inda yaro daya ke mutuwa cikin dakikoki 30 a kullum.

Malaria tana kashe mutane akalla 800,000 a duniya duk shekara.

Kashi 90 cikin 100 na masu dauke da cutar suna yankin Afrika kudu da hamadar sahara.

Gidan sauro da maganin kashe kwari da magununan cutar malaria, in ji masana yana daga cikin abubuwan dake kara yada cutar.

Karin bayani