Turkiyya ta yi sassauci kan hana rufe kai

Wata mata da dankwali a Turkiyya
Image caption Amma masu suka na cewa hakan wata kafar ungulu ce ga dokokin tsarin rabe addini da na mulki a kasar

Kasar Turkiyya ta sassauta haramcin da ta sanya, na hana daura dankwali ko rufe kai a wajen aiki da ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati.

Sai dai hakan bai shafi jami'an soji da 'yan sanda da alkalai da kuma masu gabatar da kara ba.

Yunkurin na garombawul ne ga kare hakkin dan adam, a kokarin kasar na zama mamba a kungiyar Tarayyar Turai.

Masu goyon bayan Firai minista Tayyip Erdogan sun bayyana sassaucin da cewa, ya maido da 'yancin yin addini a kasar da kashi 98 cikin dari na mutanenta Musulmi ne.