Obama zai zabi shugabar babban banki

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaba Obama zai zabi mataimakiyar shugaban babban bankin Amurka, Janet Yellen a matsayin wacce zata gaji shugaban bankin Ben Bernanke.

Wa'adin Mr Bernanke zai kare a cikin watan Janairun shekara mai zuwa.

Masana kan harkokin bankuna sun ce Ms Yellen za ta kasance ba ma mace ta farko da zata fara shugabantar babban banki a Amurkar ba, har ma a ko ina a duniya idan 'yan majalisar dokokin Amurka suka tabbatar da zaben na ta.

Ana sa ran Ms Yellen za ta ci gaba da manufofin Mr Bernanke wanda ake yaba masa kan yadda yake tallabo tattalin arzikin Amurkar, bayan da ya samu nakasu a shekara ta 2008.

A baya dai shugaba Obama ya yi matsin lamba ga shugabannin jam'iyar Republican, da su amince da daga yawan adadin bashin da gwamnati zata iya karba, tare da gargadin cewa rashin yin hakan ka iya maida kasar cikin matsalar tattalin arziki.

Yayin da nan da kwanaki takwas ne wa'adin zai cika a Majalisar Dokokin, Mr Obama ya kara jaddada cewa rashin amincewarsu kafin ya zuwa wanna lokaci zai zubar da kimar Amurka a fadin duniya.