Afrika na da attajirai 55 - Mujalla

Babbar 'yar shugaban kasar Angola, Isabel Dos Santos
Image caption 'Yan Najeriya 20 ne a cikin jerin attajiran, 'yan Afrika ta Kudu tara sai Misirawa takwas

Wata mujalla mai suna Ventures a Najeriya, ta fitar da jerin hamshakan masu kudi 55 da tace ake da su a nahiyar Afrika.

Cikinsu har da mata uku wato wata hamshakiyar 'yar Najeriya kuma 'yar kasuwa mai hada-hadar mai da zayyanar kayan sawa, Folorunsho Alakija da mahaifiyar shugaban kasar Kenya da kuma 'yar shugaban kasar Angola.

Alhaji Aliko dangote ne na farko a jerin attajiran, inda ya mallaki sama da miliyan dubu 20 na dalar Amurka.

A watan Aprilun da ya wuce babban bankin duniya ya ce, yawan mutanen dake cikin kangin talauci ya karu a Afrika, a shekaru talatin da suka gabata daga miliyan 205 zuwa miliyan 414.