Amurka ta buga sabuwar takardar $100

Sabuwar takardar kudi ta dala 100 na Amurka
Image caption Kudin na takarda ne ba na roba ba ne, kuma an fara amafani da shi a ranar Talata

Kasar Amurka ta fara amfani da sabuwar takardar kudi ta dala 100, wanda babban bankin kasar ya sake tsarawa domin gujewa yin jabunta.

Takardar dala 100, ita ce kudin da aka fi yin boginta a fadin duniya, kuma Amurka ta shafe shekaru tana sake tsara ta tare da kwashe wasu shekarun tana duba yadda za a buga kudin.

A karshe sabuwar takardar kudin ta kunshi wani zare da aka daura mata, kuma lambar 100 dake jiki ya kan sauya ya zama kararrawa, ko da yake ya danganta da yadda ka juya kudin.

Haka kuma yana dauke da tambarin alkalami da kan sauya launi, amma ba a sauya wasu abubuwa ba, kamar hoton daya daga cikin wadanda suka kafa Amurka, Benjamin Franklin.