Lampedusa: Za a yi jana'izar 'yan Afrika

Image caption Mista Borosso ya sanar da baiwa Italiya dala miliyan 40, domin magance tururuwan 'yan gudun hijira

Firai ministan Italiya Enriko Letta ya ce za a yi jana'iza ta musamman, ga 'yan gudun hijiran Afrika da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin ruwa a kusa da tsibirin Lampedusa.

Lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da masu kaura 270 daga Afrika a makon jiya.

Mista Letta na ziyarar tsibirin tare da shugaban hukumar tarayyar Turai, Jose Manuel Barroso.

Tawagar ta gana da 'yan gudun hijiran kuma sun ziyarci wajen ajiye jiragen sama, inda aka ajiye akwatunan gawwakin wadanda suka mutu.