Rundunar tsaro ta kai samame a Kano

Rundunar tsaro t JTF ta baje makaman da ta samu a gidan
Image caption An samu bindiga da albarusai da ababen hada abubuwa masu fashewa da wasu radiyon oba-oba

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta JTF a jihar Kano a Najeriya ta ce, ta kai samame unguwar Gunduwawa, bayan ta samu bayanan sirri kan wasu mutane da ke zaune a wani gida da ta ke zargin 'yan ta'adda ne.

Kwamandan runduna ta uku ta sojan Najeriya Birgediya Janar Ilyasu Isa Abba ne ya jagoran rundunar tsaron, ya ce ba a kama kowa ba, amma an samu makamai a gidan.

Mazauna unguwar dake karamar hukumar Gezawa sun ce tun misalin karfe biyu na daren ranar Litinin ne, su ka dinga jin aman bindigogi har zuwa wayewar garin Talata.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa, kimanin wata daya da ya wuce ne mutanen da ake zargin suka kama hayar gidan.

Karin bayani