'Yan gudun hijiran Najeriya na cikin kunci'

Dakarun sojin Nijar na rangadi a mota
Image caption Dubban 'yan gudun hijira ne daga Najeriya ke zaman mafaka a Nijar

A jamhuriyar Nijar kungiyar agaji ta Red Cross ta duniya ta ce dubban 'yan gudun hijiran Najeriya da samu mafaka a yankin Boso na jahar Diffa na cikin mawuyacin hali.

Da dama daga cikinsu na rayuwa ne da dan taimakon da suke samu daga jama'ar da suka ba su mafaka da kungiyoyin agaji a kasar ta Nijar.

Tun a watan Mayun da ya gabata ne ake ci gaba da samun kwararowar dubban jama'a daga jahohin Borno da Yobe na Najeriya masu makwabtaka da jahar ta Difa sakamakon tashe-tashen hankulan da ake yi a can.

Tun bayan sanya dokar ta baci a jihohin Yobe da Borno da Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ake samun 'yan gudun hijiran dake tserewa zuwa kasashen Kamaru da Chadi da kuma Nijar din.