Chif Solomon Lar ya rasu

Solomon Lar
Image caption Solomon Lar ya rasu a Amurka

Tsohon shugaban jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya, Cif Solomon Lar, ya rasu.

Wani mai bai wa Cif Lar shawara ya tabbatar wa BBC cewa Mista Lar ya rasu ne a wani asibiti da ke Amurka, inda ya yi jinya.

A wata sanarwa da jam'iyyar PDP ta fitar ta hannun kakakinta, Olisa Metuh, ta ce ta kadu da jin labarin mutuwar Mista Lar, tana mai yin ta'aziyya ga iyalansa da kuma 'ya'yan jam'iyyar baki daya.

Mista Metuh ya ce Solomon Lar, wanda shi ne gwamnan jihar Filato na farko mai cikakken iko, ya kwashe rayuwarsa ne wajen ganin tabbatuwar mulkin dimokradiya.

Karin bayani