Taliban ta shimfida sharrudan tattaunawa

Hakimullah Mehsud
Image caption Shugaban Taliban a Pakistan

A wata hira ta musamman da BBC, jagoran kungiyar Taliban a Pakistan, Hakimullah Mehsud, ya ce a shirye yake ya shiga tattaunawa da gwamnati.

Sai dai Malam Hakimullah ya zayyana wasu sharuda, ciki har da kawo karshen hare hare da jirage marasa matuka da Amurka ke kaiwa, da shimfida shari'ar Musulunci.

Ya kuma ce kungiyarsa zata ci gaba da kai hare hare a kan Amurkawa da abokan kawancensu.

Hakimullah Mehsud ya zamo jagoran kungiyarsa ne bayan kashe shugabanta, Baitullah Mehsud, a wani harin jirage marasa matuka da Amurka ta kai a 2009.