Takaddama kan zaben kananan hukumomi a Yobe

Zabe a Najeriya
Image caption Zabe a Najeriya

A jihar Yobe da ke arewa-maso-gabashin Najeriya, jam'iyyar adawa ta PDP ta koka da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na tsayar da ranar gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar .

Jam'iyyar PDP ta ce ba dai-dai ba ne a gudanar da zaben a halin da jihar ke ciki na tabarbarewar tsaro, inda ta ke zargin gwamnatin APC mai mulkin jihar da cewa tana kokari ne kawai ta shirya magudi.

Sai dai a nata bangaren, gwamnatin jihar ta ce da amincewar wakilan dukkan jam'iyyun siyasar jihar aka tsayar da watan Disamba mai zuwa domin yin zaben.

A yawancin jihohin Najeriyar ba a yi zaben kananan hukumomi ba, sai kantomomin riko da ake nadawa.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba