Birtaniya za ta hana baki mallakar gida

Image caption Firaministan Birtaniya, David Cameron

Gwamnatin Birtaniya ta ce zata bullo da wata doka wadda ta yi ikirarin za ta hana wa bakin haure mallakar gida a Birtaniya.

Haka nan kuma dokar zata tilastawa wasu bakin masu izinin zama biyan kudade domin kula da lafiyarsu.

Gwamnatin ta ce tana yin hakan ne domin rage sha'awar da Birtaniya ke baiwa bakin haure da kuma yin adalci ga mutanen da ke zaune a kasar.

Karin bayani