Mutane hamsin sun mutu a Afrika ta tsakiya

Seleka rebels
Image caption Seleka rebels

Akalla mutane hamsin ne aka san sun mutu a fadan da ya barke a Jamhuriyar Afurka ta tsakiya ranar talata.

Shugabannin coci a kasar sun shaidawa BBC cewa, su na tsammanin adadin mutanan da suka mutun zai kai dari da saba'in da biyar.

Fadan ya barke ne a garin Gaga dake arewa maso yammacin kasar tsakanin tsaffin 'yan tawayen Seleka da kungiyoyin 'yan kato da gora na garin.

Ranar alhamis ne Faransa za ta gabatarwa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya wani kuduri na tura dakarun wanzar da zaman lafiya kasar.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba