An sako Firai Ministan Libya

Ali Zeidan
Image caption Firayi Ministan Libya

Rahotanni daga Libya sun ce tsaffin 'yan tawaye sun sallamo tsohon Firai Ministan Libya Ali Zeidan.

Wata majiya da ta fito daga jami'an tsaro da kuma wani dan majalisar dokokin Libya sun ce an sallamo Firai Ministan.

Tun farko dai an yi awon gaba da Firai Ministan ne daga dakin otal din sa a safiyar Alhamis.

'Yan bindiga ne suka afka cikin otal din da Ali Zeidan ya ke zama inda suka sace shi.

Wata kungiyar sojan sa kai da ke da alaka da gwamnati ce ta ce ta kama Firai Ministan, saboda wani sammaci na kama shi.

Ministan shari'a da babban mai shigar da kara na gwamnati sun ce babu wani sammaci na kama Ali Zeidan.