Tarrayar Turai ta baiwa Malala kyauta

Image caption Malala Yousafzai

Yarinyar nan 'yar Pakistan, Malala Yousafzai, wadda a bara 'yan Taliban suka harbe ta a ka, ta sami kyautar da Tarayyar Turai ke bayarwa a kowace shekara, ga mutumen da ya nuna hazaka wajen kare hakkin bil'adama.

'Yan Taliban sun harbe ta ne saboda gwagwarmayar da take yi ta ganin yara mata sun yi karatu.

Da yake sanar da kyautar, shugaban majalisar dokokin Turai, Martin Schulz ya ce, duk wanda ya san labarin Malala, ya kuma ga yadda wannan 'yar karamar yarinya ta cigaba da fafutuka bayan ta murmure, zai yaba mata sosai.

A duk shekara Majalisar Turai na bayar da Kyautar Sakharov, domin tunawa da masanin kimiyyar nan na Rasha, kuma mai fafutuka, Andrei Sakharov.

Karin bayani