Safarar 'yan Najeriya zuwa Birtaniya

Jami'an shige da ficen Birtaniya
Image caption Jami'in shige da ficen Birtaniya

Kididdiga ta nuna cewa 'yan Najeriya sun fi yawa, a cikin mutanen da ake mikawa hukumomi saboda an yi fataucinsu zuwa Birtaniya.

Alkaluman da shafin intanet mai bincike na Exano ya samu, sun nuna cewa Birtaniya ta bayar da viza ga 'yan Najeriya fiye da dubu 500, tsakanin 2009 zuwa 2012, amma kashi daya kawai cikin dari aka yiwa tambayoyi kafin a basu viza.

Alkaluman ma'aikatar cikin gida ta Birtaniya sun nuna cewa, a bara kadai hukumar shige da ficen kasar ta bayar da viza ga 'yan Najeriya dubu 126 da 487, to amma masu neman visa 553 ne kawai aka yiwa tambayoyi.

Dan majalisa

A cewar shafin internet na eXARO Shugaban jam'iyar Conservative a majalisar birnin London, Andrew Boff wanda ke bincike kan fataucin mutane, yace alkaluman da shafin ya bankado sun girgiza shi.

Ya kuma ce wannan ne yasa masu fataucin mutane ke ta kara son zuwa Birtaniya, wadda ake ganin wata kofa ce ta shiga Turai.

Ya ce babu wadatattun hanyoyin bincike, abin da ke sa ana fataucin mutane marasa galihu, wadanda kuma ake zargin ana tilasta musu yin karuwanci.

Amfani da tsafi

Daya daga cikin wadanda aka yi fataucinsu ta shaida wa EXaro cewa, an yi mata alkawarin kyakykyawar sabuwar rayuwa a London, a matsayin mai gyaran gashi, amma kuma aka garkame ta a wani gida a London ana lalata da ita ba da son ranta ba.

Ta bayyana cewa an gabatar da ita ga masu fataucin mutane a Lagos Najeriya, inda suka yaudari jami'an Birtaniya suka ba ta viza.

Ta ce wata rantsuwa ta tsafi ce ta daure ta ga wadanda suka yi fataucinta.

Masu fafutuka dai na sukar hukumar shige da ficen Birtaniya da hukumar kula da manyan laifuka, da gaza yin wani shirin da zai mayar da hankali a kan wadanda abin ya shafa.