Amurka za ta dakatar da taikamakon soji a Masar

Dakarun Amurka a kasar Masar
Image caption Dakarun Amurka a kasar Masar

Amurka ta bayyana cewa zata dakatar da taimakon sojin da take bai wa kasar Masar har sai ta ga an samu cigaba ta fuskar dimokradiyya.

Wannan mataki dai zai shafi bayar da jiragen yaki,makaman kare dangi da jirage masu saukar angulu, dama tsabar kudi dala miliyan sittin.

Amurkar dai za ta ci gaba da bayar da tallafi a bangaren kiwon lafiya, ilmi da yaki da ta'addanci ga kasar ta Masar.

Mai magana da yawun ofishin huddar jakadancin Amurkar Marie Harf ta ce, wannan mataki da shugaba Obama ya bada umarni a kai ya karkare da cewa Amurka na bukatar sake auna mizanin irin tallafin da take bayar wa.

Bayan farmakin soji kan 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ne a cikin watan Ogusta ne Amurkar ta dakatar da bayar aikewa da kananan jiragen yaki masu kirar F-16 da kuma soke batun atisayen sojin na hadin guiwa da kasar ta Masar.