Kwalara ta kashe mutane 96 a Zamfara

Wasu yara na diban ruwa
Image caption Ruwa da abincin da ya gurbata da kwayar cutar kwalara na kaiwa ga kamuwa da cutar

Kimanin mutane 96, mafi yawansu yara ne sun rasa rayukansu a sanadiyyar barkewar cutar kwalara a jihar Zamfara a Najeriya, acewar kungiyar likitoci masu bada agaji.

Mutanen sun mutu ne cikin makonni biyu da barkewar cutar a jihar, yayin da wasu sama da 500 da cutar ta kama ke karbar magani a asibitoci.

An danganta barkewar cutar da shan gurbataccen ruwa a garuruwan Maradun da Anka da Bungudu da kuma Gusau babban birnin jihar.

A jihar ta Zamfara ne aka samu barkewar cutar gubar dalma, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar yara 400 a 'yan shekarun baya.

Karin bayani