Tsohuwar ministar Ilimin Najeriya

Image caption Rukayyatu ta taka rawar wajen bai wa mata Ilimi

An haifi Farfesa Rukayyatu Ahmed Rufai a garin Ringim na jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya.

Ta yi karatun Digirinta na farko a fannin Tarihi a Jami'ar Bayero da ke Kano a shekarar 1981.

Haka kuma ta yi Digiri na biyu a Jami'ar ta Bayero a shekarar 1987.

Daga nan ne kuma ta tafi Amurka inda ta yi karatun Digirin Digirgir a fannin Ilimi a Jami'ar West Virginia University da ke Amurka a shekarar 1991.

An nada Farfesa Rukayyatu Rufai a matsayin Kwamishiniyar harkokin Lafiya ta jihar Jigawa daga shekarar 1993 zuwa 1996.

Ta zama Farfesa a shekarar 2003, sannan ta sake rike mukamin Kwamishiniyar Ilimi da Kimiyya da Fasaha a jihar Jigawa.

A shekarar 2010 ne mukaddashin shugaban Najeriya a wancan lokacin, Dr Goodluck Jonathan, ya nada ta a matsayin Ministar harkokin Ilimi ta kasar.

A watan Satumba na shekarar 2013 shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya sallami wadansu ministoci daga cikin gwamnatinsa, cikinsu har da Farfesa Rukayyatu Rufai.

Karin bayani