AU ta cimma matsaya a kan kotun duniya

Taron kungiyar Afrika
Image caption Taron kungiyar Afrika

Shugabannin kasashen Afirka dake taro a Ethiopia sun cimma matsayar cewa, ba wani shugaban kasar Afirka da zai gurfana a gaban duk wata kotun duniya nan gaba.

Kungiyar AU ta kuma bukaci Kenya ta rubutawa kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya wasikar neman a dakatar da shari'ar da ake yi wa shugabannin Kenya.

Taron kungiyar a Addis Ababa ya amince da kara yawan sojojin da ya ke samarwa a Somaliya da kashi daya bisa uku domin kara kaimi wajen yaki da 'yan kungiyar Al-Shabaab.

A cikin wata sanarwa, kungiyar ta ce za ta kara yawan sojojinta da ke Somaliya zuwa fiye da dubu shida, wanda idan aka hada da wadanda ke can a yanzu za su kai kusan dubu ashirin da hudu.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba