An kashe mutane 16 a garin Barikinladi

Wasu dakarun sojin Najeriya
Image caption Batun matsalar tsaro na cigaba da ciwa mutane da dama tuwo a kwaraya a Najeriya

Rundunar 'yan sanda ta jihar Plato ta tabbatar da mutuwar mutane 16 a wani harin da aka kai a barikin ladi a ranar Alhamis.

Kakakin rundunar felicia Anselem ce ta tabbatar wa da BBC hakan, inda ta ce wasu barayin shanu ne suka ka kai harin.

Ko da yake wasu rahotanni na cewa mutane 21 ne suka mutu.

Kakakin ta bayyana cewa barayin sun kashe wani mutum da iyalinsa su 10, yayin da kuma 'yan banga sun kashe barayin su 6.