Giwaye na fahimtar nuni da hannu - Bincike

Wata giwa cikin wadanda aka yi binciken a kai
Image caption Wata giwa cikin wadanda aka yi binciken a kansu

Wani sabon bincike ya nuna cewa, giwaye na fahimta idan aka yi musu nuni da hannu, ba kamar sauran dabbobi ba.

An yi binciken ne a kan wasu giwayen da ake kiwo a kasar Zimbabwe, inda masu binciken suka gano cewa, suna banbance bokitin dake cike da abinci da kuma wanda babu komai.

Farfesa Richard Byrne, wanda ya jagoranci binciken daga jami'ar St. Andrews ta Scotland, ya ce giwayen kamar mutane sun san amfanin nuni da hannu.

Musamman a tsakanin al'ummar dake bukatar goyon baya da kuma taimakon juna a rayuwa, a cewar farfesa Byrne.