Ana bikin ranar yara mata ta duniya

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya
Image caption Ofishin Majalisar Dinkin Duniya

Yau ake bikin ranar yara mata ta duniya, wacce majalisar dinkin duniya ta ware domin nazari kan al'amuran da suka shafi yara matan.

Rana ce da ake nuna goyon baya ga bai wa 'yaya mata damar samun ilimi da kuma kara fadakar da al'umma irin rashin daidaiton da suke fuskanta a ko'ina a duniya.

Hakan dai ya hada da na fannin samun ilmi da ciyarwa da kula da lafiyarsu da kuma kare su daga nuna wariya.

A karo na biyu da ake bikin, na wannan shekarar ta 2013 zai maida hankali wajen fito da wasu sabbin hanyoyin habbaka ilmin 'ya'ya matan.

Sai dai ta ce yayin da aka sami ci gaba sosai wajen bude kofofin samun ilmi ga 'ya'ya mata, a cikin shekaru 20 da suka gabata, ana ci gaba da hana 'ya'ya mata da yawa wannan damar.