Kenyatta ya bukaci a dakatar da shari'arsa

Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta

Lauyoyin Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, sun bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta duniya -ICC su ajiye tuhumar da suke yi wa shugaban, tun kafin a soma shari'ar.

A wata wasika da suka aikawa kotun dake Hague, Lauyoyin sun ce suna da hujjojin dake nuna cewar an nunawa shaidu fin karfi.

A cewarsu, masu shigar da kara suna kokarin kawar da abubuwan da suka shafi adalci a shari'ar.

'Rikicin bayan zaben'

Ana zargin Mista Kenyatta da cin zarafin bil adama lokacin da aka yi tashin hankali bayan zaben 2007 a kasar, inda mutane 1,200 suka mutu sannan wasu kusan 600,000 suka rasa matsugunansu.

Amma dai ya musanta wannan zargin.

Ana saran soma shari'ar Mista Kenyatta a ranar 12 ga watan Nuwamba a Hague.

Tuni Mataimakin shugaban kasar, William Ruto ya bayyana gaban kotun don kare kansa bisa zargi da hannu a kashe-kashen.