INEC ta ce Bamanga ne shugaban PDP

Alamar jam'iyyar PDP
Image caption 'Yan Najeriya da dama za su zuba ido su ga mataki na gaba da bangaren Baraje za su dauka

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, ta tabbatar da Alhaji Bamanga Tukur a matsayin shugaban jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

Hakan na kunshe ne a wata wasika da hukumar ta aike wa shugaban PDP da ta balle Abubakar Baraje, bayan sun bukaci hukumar ta tabbatar da shi a matsayin shugaban PDP.

INEC ta ce ta sa ido a zaben jam'iyyar da aka yi a watan Maris na bara, wanda aka zabi Bamanga a matsayin shugaban jam'iyyar, saboda haka ba zai yiwu hukumar ta amince da wani ba.

Har ila yau a ranar Alhamin ne kuma, wata kotu a jihar Legas ta yi watsi da karar da bangaren Barajen ya shigar, na kalubalantar Bamanga Tukur, a bisa dalilin cewa ba ta da hurumin sauraron karar.