Za a ba da lambar zaman lafiya ga OPCW

Ofishin hukumar hana bazuwar makamai masu guba a duniya
Image caption Ofishin hukumar hana bazuwar makamai masu guba a duniya

Za a bada lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya ta wannan shekara, ga hukumar hana bazuwar makamai masu guba, wacce ke lalata makaman kasar Syria.

Kwamitin bada labar da ya sanar da hakan a birnin Oslo na Norway ya yabi hukumar game da aiki tukuru na kawar da makamai masu guba.

Daraktan hukumar Ahmet Uzumcu, ya ce hari mai tada hankalin da aka yi da makamai masu guba a Syria, na tunatar da cewa akwai sauran rina a kaba.

Hukumar dai ta sa ido wajen lalata kusan kashi 80 cikin dari na makamai masu guba a duniya, tun bayan kafa ta a shekarar 1997.