'Yan Republican sun gana da Obama

Shugaban Amurka Barak Obama
Image caption Shugaban Amurka Barak Obama

'Yan jam'iyar Republican a majalisar dokokin Amurka sun gana da shugaba Obama kan yarjejeniyar kawo karshen takaddamar dake faruwa.

Duka bangarorin sun bayyana ganawar ta sa'a daya da rabi a matsayin mai amfani.

Amma ba a tsaida magana kan shawarar da 'yan jam'iyar Republican suka bayar ba, kan kara yawan kudaden bashin da gwamnati za ta iya karbowa na wucin gadi ba.

Za a cigaba da tattaunawa, kana 'yan jam'iyar Republican sun bukaci shugaba Obama da ya amince da kara zaman sasantawa kan takaddamar kasafin kudin da ta tilasta rufe wasu ayyukan gwamnati tun ranar daya ga watan Oktoba.

Shugaban masu rinjaye kuma dan jam'iyar Republican a majalisar dokokin, Eric Cantor ya ce "Shugaba Obama ya ce zai tuntubi 'yan majalisar gudanarwar gwamnatinsa, yana mai fatan za a samu ci gaba bayan hakan.''