Mahaukaciyar guguwa a Indiya

India
Image caption An kwashe dubban jama'a saboda fargabar mahaukaciyar guguwar

Daya daga cikin mahaukaciyar guguwa dake tafiya da ruwa da ta shafi India na dosar gabar tekunta ta gabas a inda ake sa ran nan gaba kadan za ta shafi yankunan doron kasa.

Tuni dai mutane fiye da dubu 440 suka bar kasarsu domin tsere wa mahaukaciyar guguwar Phailin a mashigin ruwan Bengal.

An bukaci duk wasu mazauna kauyuka da masuntan da suka rage a yankin da su bar garin Gopalpur na gabar teku dake a Orissa, a inda tuni iska ke kadawa da karfin iya cin kilomita kusan 200 a cikin sa'a guda.

Sai dai jami'ai sun ce sun shirya tsaf wajen tunkarar wannan bala'i

Irin wannan iska mai karfi dai a shekarar 1999 ta kashe mutane fiye da dubu goma a jahar Orissa.

Karin bayani