"Babu adalci wajen daukar daliban soji"

Sultan Sa'ad Abubakar
Image caption Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar

A Najeriya, Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci da kuma majalisar malamai da limamai ta kasar sun nuna damuwa dangane da yadda ake daukar dalibai a makaranta horas da hafsoshin soji a kasar, lamarin da suka ce na barazana ga hadin kan al'umma.

A cewarsu, bisa bayanan da suka samu, akwai rashin adalci a yadda ake daukar dalibai da suka fito daga wasu jihohin kasar a makarantar sojin.

A karshen wani taro da suka kammala a Kaduna, malaman sun kuma bukaci hukumomin kasar da su tabbatar da ganin a tattauna tare da fadakar da malaman addini kan allurar rigakafin cutar shan inna wato Polio.

A cewarsu, hakan zai taimaka wajen kawo karshen kyamar da wasu ke nuna wa rigakafin cutar ta shan inna.

Har ila yau, malaman sun kuma yaba wa gwamnatin jihar Kaduna kan irin matakan da ta dauka na hana barkewar rikicin addini a garin Kafanchan dake Kudancin jihar.

Karin bayani